Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka# Sin na da imanin warware matsala
2019-06-02 12:27:45        cri

Gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani a yau Lahadin cewa, kome canzawar yanayin da ake ciki, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan gudanar da harkokin kanta yadda ya kamata. Kasar Sin dake bude kofarta ga waje za ta yi kyakkyawar mu'amala tare da duniya, lamarin da zai kyautata Sin da duniya baki daya.

Takardar bayanin ta kuma nuna cewa, raya kanta ta hanyar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje muhimmiyar hanya ce ga kasar Sin wajen tinkarar takaddamar ciniki a tsakaninta da Amurka. Sin za ta ci gaba da zurfafa aikin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, da ma daukar jerin muhimman matakai, ciki har da amincewa da shigowar jarin waje a fannoni masu yawa, da kara hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen kiyaye ikon mallakar ilmi, da kara shigo da kayayyaki da ayyukan ba da hidimar kasuwar Sin, da dai sauransu.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China