2019-06-02 12:08:03 cri |
Sin ta jaddada a cikin takardar bayanan gwamnatin da aka fitar a wannan rana cewa, ko da yaushe Sin na tsayawa tsayin daka kan cika alkawarinta, da nuna sahihanci ga gwamnatin kasar Amurka wajen yin tattaunawar ciniki a tsakaninsu. Sin na dora muhimmanci ga batutuwan da Amurka take sa lura a kai, da yin kokarin neman hanyoyin daidaita matsalolinsu. Bangarorin biyu sun samu babban ci gaba kan tattaunawar ciniki a tsakaninsu a zagaye 11, wanda ya dace da moriyar Sin da Amurka, kyakkyawan sakamakon da bangarorin biyu suka yi kokarin cimmawa. Sin ta cika alkawarinta a wajen tattaunawar, kana ta jaddada sau da dama cewa, idan bangarorin biyu suka cimma yarjejeniyar, Sin za ta cika alkawarinta da aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata. (Zainab)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China