Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka# Ya kamata shawarwari a tsakanin Sin da Amurka ya dora muhimmanci kan babbar moriyar juna
2019-06-02 12:07:46        cri

Kasar Sin ta jaddada a yau Lahadi cewa, ya kamata shawarwari a tsakanin Sin da Amurka ya girmama juna da zaman daidai wa daida da moriyar juna. Ko da yaushe kasar Sin ta dukufa wajen daddale yarjejeniyar da dukkan bangarorin biyu za su amince da ita. Idan wani sashi ya tilastawa wani wajen yin shawarari, ko sakamakon shawarwarin zai amfanawa sashi daya kadai, to dole ne shawarwarin ba zai cimma nasara ba.

A cikin takardar bayani mai taken "matsayin Sin kan shawarwarin ciniki a tsakanin Sin da Amurka" da gwamnatin kasar Sin ta bayar, an jaddada cewa, ma'anar girmama juna ita ce nuna girmamawa ga tsarin mulkin juna, tsarin tattalin arzikin juna, hanyoyi da hakkin raya kasarsu, da ma babbar moriyar juna. Kada a nemi cin moriyar wata kasa, har ma a lalata ikon mulkin wata kasa a cikin shawarwarin.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China