Tuesday    Apr 8th   2025   
in Web hausa.cri.cn
An wallafa littafin da shugaba Xi Jinping ya rubuta na harshen kasar Kyrghyzstan
2019-06-09 16:57:04        cri

An yi bikin wallafa littafin da shugaba Xi Jinping ya rubuta mai taken "Kalaman Xi Jinping kan mulkin kasa da tafiyar da harkokin kasa" babi na daya na harshen kasar Kyrghyzstan kuma taron tattauna dabarun gudanar da harkokin kasa tsakanin Sin da Kyrghyzstan wanda aka yi a jiya a fadar shugaban kasar Kyrghyzstan dake Bishkek. Shugaban kasar Kyrghyzstan Sooronbay Zheenbekov, tsohuwar shugabar Kyrghyzstan Roza Otumbaeva, mataimakin shugaban sashen yayata ayyuka na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Wang Xiaohui, jakadan Sin dake Kyrghyzstan Du Dewen sun halarci biki tare da gabatar da jawabai.

A cikin jawabinsa, shugaba Sooronbay Zheenbekov ya ce, Mista Xi daya ne daga wasu manyan 'yan siyasa dake da martaba mafiya karfi a yanzu a duniya har wasu lokutan masu zuwa nan gaba, littafin da ya rubuta ya yi bayani kan bunkasuwa cikin sauri da Sin ta samu a baya, kuma ya yi hangen nesa kan hanyoyi da kuma matakan da Sin za ta bi nan gaba, kana kuma, ya bayar da ra'ayin Sin kan kalubalen da duniya ke fuskantar yanzu ta fuskar tattalin arziki, tsaro, muhallin halittu da dai sauransu. Za a iya fahimtar tunanin shugaba Xi da ka'idojin JKS, da kuma sanin yadda kasar Sin ke samun bunkasuwa da hanyoyin da take bi da kuma ci gaban da take samu ta hanyar karanta wannan littafi. A cewarsa, la'akarin da kwaskwarima da kasar take yi kan siyasa, tattalin arziki da doka da kuma sa kaimi ga raya matakan gudanar da harkokin kasa na zamani, wannan littafi zai ba da haske ga 'yan siyasa da jami'an kasar da sauran manazarta, kowa zai kara ilminsa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China