Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Sin na mai da hankali kan hadin gwiwar kasa da kasa domin samun dauwamammen ci gaba
2019-06-08 18:15:35        cri

Jiya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi yayin taron tattauna tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Saint Petersburg na Rasha, inda ya bayyana cewa, bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, har kullum kasar Sin ta nace ga cika alkawarin da ta dauka, a fannin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa domin samun dauwamammen ci gaba, makasudin gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya a shekarar 2013, shi ne domin sa kaimi kan ci gaban kasa da kasa.

Xi ya kara da cewa, an shirya taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2 a birnin Beijing cikin nasara, inda sassa daban daban suka amince cewa, za su nace ga maradun bude kofa da kiyaye muhalli da hana cin hanci da rashawa domin cimma burin kyautata rayuwar jama'a tare kuma da samun dauwamammen ci gaba bisa tushen tattaunawar juna da moriyar juna, kana za a hada shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar MDD waje guda, ta yadda za a daidaita huldar dake tsakanin tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma muhalli cikin lumana, a karshe za a cimma burin samun dauwamammen cigaba a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China