Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Dauwamammen ci gaba zai sa a samu karin moriya
2019-06-08 18:08:36        cri

Jiya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi mai taken "Nace ga manufar samun dauwamammen ci gaba domin kago duniya mai wadata" yayin taron tattauna tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Saint Petersburg na Rasha, wanda ke da taken "Tsara ajandar samun dauwamammen ci gaba", inda ya bayyana cewa, babban taken taron ya dace da yanayin da kasashen duniya ke ciki a yanzu, a don haka yana da babbar ma'ana, a halin da ake ciki yanzu, yanayin duniya yana samun manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru dari daya da suka gabata, ya dace ya yi hadin gwiwa, ajandar samun dawwamammen cigaba nan da shekarar 2030 ta MDD ta fi mai da hankali kan batutuwa guda uku wato karuwar tattalin arziki da bunkasuwar zaman takewar al'umma da kuma kiyaye muhalli, batutuwan da zasu kawowa al'ummomin duniya makoma mai haske.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China