![]() |
|
2019-06-09 16:08:45 cri |
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Lu Kang ya sanar a yau 9 ga wata cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Kyrgyzstan daga ran 12 zuwa 14 ga watan nan, bisa gayyatar da takwaransa Sooronbay Zheenbekov ya yi masa, tare da halatar taron majalisar shugabannin kasashe mambobin SCO karo na 19.
Ban da wannan kuma, bisa gayyatar shugaban kasar Tajikistan Emomali Rakhmonov, shugaba Xi zai halarci taron koli karo na 5 kan matakin hadin kai da aminci da juna tsakanin kasashen Asiya tare da ziyarar aiki a kasar daga ranar 14 zuwa 16 ga watan nan na Yuni. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China