Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Sin na son kokari da sauran kasashe domin samun dauwamammen ci gaba
2019-06-08 18:20:35        cri

Jiya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi yayin taron tattauna tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Saint Petersburg na Rasha, inda ya bayyana cewa, burin samun dauwamammen ci gaba buri ne na yawancin kasashen duniya, ba zai yiwu ba a hana yunkurin, kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran kasashen duniya domin daukan hakikanan matakai tare dasu, ta yadda za a cimma burin samun dauwammamen ci gaba, kuma kasar Sin za ta cigaba da nacewa ga manufar tattaunawa tare da ginawa tare da kuma samun moriya tare, domin gina tattalin arzikin duniya da zai dace da yanayin daukacin kasashen duniya, kana za ta kara mai da hankali kan moriyar al'ummomin kasashen duniya domin samar da alheri gare su, a don haka ya dace mu nace ga manufar raya tattalin arziki bisa tushen kiyaye muhalli, tare kuma da tabbatar da zaman jituwa dake tsakanin bil Adama da hallitu masu rai da marasa rai.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China