Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ana bukatar abokai wajen yin hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa
2019-06-08 18:37:38        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a gun taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin kasa da kasa da aka gudanar a birnin St. Petersburg a jiya cewa, ana bukatar abokai masu yin imani da juna dake da buri iri daya wajen yin hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, kasar Rasha muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ce dake kan matsayin gaba yayin da take yin hadin gwiwa dake tsakaninta da Sin a fannoni daban daban. Bangarorin biyu sun bi tunanin samun bunkasuwa mai dorewa, da yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin makamashi mai tsabta kamar iskar gas, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da tattalin arzikin sadarwa, da ciniki ta yanar gizo, da yin amfani da albarkatunsu a fannoni daban daban da sauransu. Sin da Rasha sun cimma daidaito kan hadin gwiwar raya shawarar "ziri daya da hanya daya" da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya. Hakazalika, raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ya yi daidai da tunanin raya dangantakar abokantaka a tsakanin Turai da Asiya da shugaba Putin ya gabatar, don haka ana iya nuna goyon baya ga juna, da sa kaimi ga raya su tare, hakan zai sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arziki a yankin, da kuma cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China