Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Sin na son amfanin sabbin sakamakon ci gaba da sauran kasashe
2019-06-08 18:28:49        cri

Jiya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi yayin taron tattauna tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Saint Petersburg na Rasha, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da kara bude kasuwarta ga kamfanonin ketare, ta yadda zata samar da muhallin kasuwa mai inganci gare su, za ta kuma ci gaba da sanya kokari domin ingiza cudanyar tattalin arzikin duniya, tare kuma da kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban, da daidaita matsalar rashin daidaiton cigaban tattalin arzikin duniya, tana son gudanar da hadin gwiwar cinikayya dake tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa tushen daidai wa daida da martabar juna, ta yadda za a cimma burin samun moirya tare, ban da haka kasar Sin tana fatan za a samar da karin damammaki ga kasashe masu tasowa ta hanyar kafa asusun samar da tallafi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da asusun shimfida zaman lafiya da tabbatar da zaman lafiya na kasar Sin da MDD. Haka zalika kasar Sin tana son amfanin sabbin sakamakon kimiyya da fasaha dake kumshe da fasahar 5G tare da sauran kasashen duniya, ta yadda za a gudanar da gogayya mai inganci tsakanin kasa da kasa tare kuma kyautata tsarin karuwar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

Shugaba Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana fatan kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya a bangarorin yaki da talauci da samar da tabbaci ga zamantakewar rayuwar al'umma domin kawo alheri ga daukacin al'ummomin kasashen duniya baki daya, kana za ta kara mai da hankali kan aikin kiyaye muhalli domin dakile matsalar sauyin yanayi tare da sauran kasashen duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China