Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Sin a shirye take ta hada gwiwa da kasa da kasa don tabbatar da zaman lafiyar duniya
2019-06-08 17:49:51        cri
A ranar 7 ga wata, yayin da Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ke ba da jawabi a yayin taron SPIEF, ya bayyana cewa, a yayin da kasashen duniya ke cigaba da fuskantar sabbin sauye sauye da kalubaloli, zaman lafiya da samun dauwamamman cigaba su ne muhimman abubuwan da suka fi muhimmanci ga duniyar da muke ciki a halin yanzu, yayin da ko wace kasa da ko wace al'umma ke fuskantar batutuwa marasa tabbas kuma mabambanta.

Kasancewar duniya na kan wani matsayi da take neman tsallake shi a bisa tarihi, akwai bukatar tattara tunani da basirar dukkan bil adama domin yin hadin gwiwa don cimma nasarar samun sakamako karkashin mu'amalar hadin gwiwa ta moriyar juna, kuma wannan shi ne zabi mafi dacewa da ya kamata a dauka don shawo kan kalubalolin dake fuskantar kasa da kasa, Xi ya bayyana cewa, samar da dauwamman cigaba shi ne ginshike warware matsalolin dake addabar duniya.

Xi ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da dukkan bangarori wajen tabbatar da samun dauwamamman cigaban duniya, kuma za ta sauke nauyin dake bisa wuyanta na gina al'umma, da samar da kyakkyawar makoma ga bil adama a nan gaba, da tabbatar da hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa, da inganta tsarin shugabancin kasa da kasa, da nufin samar da cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, da samar da yanayin mafi inganci ga duniya baki daya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China