Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu Gabatar Da Shirin Telabijin Na Sin Da Amurka Sun Yi Muhawara
2019-05-30 15:19:40        cri

 

A karfe 8 da minti 25 a safiyar yau Alhamis, bisa agogon Beijing, kwatankwacin karfe 8 da minti 25 a daren ranar 29 ga wata, bisa agogon gabashin Amurka, mai gabatar da shiri na gidan telabijin din kasar Sin CGTN, Liu Xin, ta yi wata muhawara a bainar jama'a da takwararta ta kafar kasuwanci ta gidan telabijin din Fox na kasar Amurka, Trish Regan, kan maganar ciniki tsakanin Sin da Amurka, gami da sauran batutuwan da suka shafi kasashen 2.

Liu Xin ta halarci muhawarar ne bisa gayyatar da Regan ta yi mata, inda ta nuna fuskarta cikin shirin da Malama Regan ke gabatarwa mai taken "Lokaci na Zinare", ta hanyar fasahar sadarwa mai amfani da tauraron dan Adam.

Wannan shi ne karon farko da wasu masu gabatar da labarai na Sin da Amurka suka yi muhawara a tsakaninsu. Malaman 2 sun kwashe minti 16 suna muhawara da juna, kana abubuwan da suka tattauna sun shafi ciniki cikin adalci, da ikon mallakar fasahohi, da maganar kamfanin Huawei, da harajin kwastam, da matsayin kasar Sin na wata kasa mai tasowa, gami da kalmar "State Capitalism" wato tsarin jarin hujja karkashin kulawar gwamnati, da kasar Amurka ke yin amfani da ita wajen siffanta tsarin kasar ta Sin.


1  2  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China