Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaba da tattauna batun cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya dogara kan halayya da gaskiyar Amurka
2019-05-31 09:54:29        cri

Ma'aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce yiyuwar ci gaba da tattauna batun cinikayya tsakanin Sin da Amurka ko kuma akasinsa, ya dogara ne kan halayya da tabbatar da gaskiya daga bangaren Amurka.

Kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, za a iya ci gaba da tattaunawa amma karkashin adalci da mutunta juna.

Ya ce halayya mara kyau daga bangaren Amurka, ta ta'azzara takaddamar cinikayya da bazuwarta zuwa wasu bangarori, abun da ya illata tubali da yanyin tattaunawar, yana mai cewa alhakin baki daya na wuyan Amurka.

Dangane da tsokacin Amurka na baya-bayan nan kan tattaunawar, Gao Feng ya ce bayanan da Amurka ke bayarwa su kan sauya, wanda alama ce ta tantamar gaskiyarta.

Ya ce Sin ta yi amana cewa hadin gwiwa ita ce zabi daya tilo gare ta da Amurka, yana mai cewa akwai ka'idojin tuntubar juna da hadin gwiwa.

Har ila yau, kakakin ya kara da cewa, bangaren kasar Sin ba zai taba amincewa da duk wata yarjejeniya da za ta illata cikakken 'yancinta da martaba ba, yana mai cewa, Sin ba za ta sadaukar da muhimman ka'idojinta ba.

Ya ce idan aka cimma matsaya, to akwai bukatar bangaren Amurka ya nuna gaskiyarsa da kuma magance muhimman batutuwan da Sin ta gabatar, tare da ci gaba da tattaunawar karkashin adalci da mutunta juna. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China