Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: imani ba ya fitowa daga karya da magagi
2019-05-31 20:49:15        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce matakan da kasar Amurka ke dauka na bin ra'ayin cin gashin kai, da na kariyar cinikayya, na gamu da adawa mai tsanani daga jama'arta, baya ga zargin da kasashen duniya ke yi mata. A nata bangaren kuwa, kasar Sin na fatan ganin Amurka ta fahimci yanayin da ake ciki, ta dakatar da muggan ayyukanta, don sake komowa hanyar da za ta dace.

Kakakin ya bayyana haka ne, a yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau Jumma'a a nan birnin Beijing.

Rahotanni sun ce a jiya Alhamis 30 ga wata, shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya ce kasarsa na tinkarar batun tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da Sin yadda ya kamata. Ya ce matakin da kasar Amurka ke dauka na kara sanya haraji kan kayayyakin da take shigowa da su daga kasar ta Sin yana yin mugun tasiri ga kasar, wanda hakan ya sanya kamfanonin kasashen ketare dake kasar Sin suke ficewa zuwa sauran kasashen Asiya. Don haka, a cewar sa yanzu kasar Sin na zama wata kasa mai matukar rauni.

Game da hakan, Geng Shuang ya ce, kasar Amurka ta sanya irin wadannan karya sau da dama, ko da yake kasar Sin ta bankado karairayin, amma kasar Amurka ta nuna tana sha'awar hakan, inda ta sake sanya karin wasu karya. Tamkar dai tana tsammanin cewa, idan ta kara sanya karya, to mutane za su kara amincewa da ita, har ma za ka iya kara imaninta. A cewar kakakin, kada kasar Amurka ta auna karfinta na kakaba karya, kuma kada ta kaskantar da kwarewar sauran sassa ta hanyar kimanta karyarta. Imani na fitowa ne daga dacewar yanayin da ake ciki.(Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China