2019-05-30 21:22:36 cri |
Da farko, martaba juna.
Wannan muhawara tsakanin Liu Xin da Trish ta yi kama da mu'amala ta zaman daidai wa daida, inda bangarorin biyu suka martaba juna. Ko da yake sun bambanta wajen matsayin da suka dauka, amma suna kuma da ra'ayi daya a kan wasu batutuwa, a yayin da suke bayyana bukatunsu na kiyaye moriyar kasashen su, a sa'i daya kuma sun bayyana fatansu na ci gaba da tattaunawa.
Na biyu, yin mu'amala cikin zaman daidai wa daida.
Wani muhimmin dalilin da ya sa aka mai da hankali sosai kan wannan tattaunawa, shi ne wadannan masu gabatar da shiri sun fito ne daga manyan kasashe biyu a duniya. Bisa yanayin da ake ciki na fuskantar takaddamar ciniki a tsakanin kasashen Sin da Amurka, abubuwan da masu gabatar da shiri suka yi tamkar sun nunawa kasashen duniya cewa, yin mu'amala cikin zaman daidai wa daida, ya fi nuna kiyayya ga juna.
Na uku, kawar da bahaguwar fahimta.
A tattaunawar da Liu Xin da Trish suka yi, ana iya gano cewa, wasu Amurkawa suna yiwa kasar Sin bahaguwar fahimta, saboda ra'ayin da aka dora su a kai tun fil azal, da ma rashin fahimta kan ainihin kasar Sin. A karshen tattaunawar, Liu Xin ta yi maraba da Trish da ta zo kasar Sin don kara fahimtar kasar, hakan na nuna cewa, 'yan jaridar kasar Sin tana maraba da abokai, da kuma niyyar kasar ta bude kofa ga kasashen ketare.(Mai fassara: Bilkisu Xin)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China