![]() |
|
2019-05-30 11:19:47 cri |
Da misalin karfe 8 da minti 25 na safiyar yau bisa agogon Beijing, wakiliyar gidan talibijin na Fox dake kasar Amurka Trish Regan, da takwararta ta gidan talibijin na kasar Sin CGTN Liu Xin, sun yi muhawara ta tsawon minti 25 a tsakaninsu dangane da kudin kwastam, da ikon mallakar ilmi da dai sauransu.
A yayin muhawarar, Trish Regan ta nuna wa Liu Xin girmamawa, Liu Xin kuma ta amsa tambayoyinta yadda ya kamata cikin nutsuwa. Amma Trish Regan ba ta san kasar Sin sosai ba, ta nuna bambanci kan kasar Sin a fannin tattalin arziki da ciniki. Wani mai sharhi na Fox ya bayyana bayan muhawarar cewa, Trish Regan ba ta yi fushi sosai ba a yau. Mutanen Sin suna da ladabi kamar yadda Liu Xin ta yi. Da wuya sosai a yi fushi da su. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China