Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin yada labarun waje sun ce, kasar Sin ta bayyana matsayinta a hukumance cikin takardar bayaninta
2019-06-03 13:35:34        cri

Jiya Lahadi ne kasar Sin ta fitar da takardar bayani a hukumance, kan matsayarta dangane da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da kasar Amurka, tare da shirya wani taron manema labaru, wadanda suka jawo hankali sosai. Kafofin yada labaru na kasashen ketare sun bada labarin cewa, a hukumance ne kasar Sin ta bayyanawa Amurka matsayinta cikin takardar bayanin. Kana jami'an Sin sun amsa tambayoyin manema labaru kan wasu al'amurran da suka jawo hankali sosai a kwanan baya.

Kamfanin dillancin labaru na Faransa wato AFP yace, kasar Sin ta bayyanawa Amurka matsayinta da gaggawa kan batun cinikayya cikin takartar bayanin, wanda ya ce, takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka ba zata sanya Amurka ta sake samun karfi ba, sai dai ma zata kawo illa ga tattalin arzikin Amurkar.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bada wasu labaru kan yadda kasar Sin ta fitar da takardar bayanin da kuma kalaman jami'an Sin a yayin taron manema labarun. Rahotanni sun ce, takardar bayanin ya yi nuni da cewa, yadda Amurka ta sanar da kara kudin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke sayarwa a Amurka, bai yi wani amfani wajen warware matsalar tattalin arziki da ake ciniki a tsakanin kasashen 2 ba. Ya kamata Amurka ta sauke nauyin kawo cikas ga tattaunawar dake tsakanin kasashen 2. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China