Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka# Cin zali a fannin cinikayya da Amurka ke yi na kawo illa ga duniya
2019-06-02 11:20:21        cri

Bisa wata takardar bayanin da gwamnatin kasar Sin ta bayar a yau Lahadi, an ce, jerin matakan bada kariya ga ciniki da Amurka ta dauka ya sabawa ka'idojin kungiyar WTO, da lahanta tsarin cinikayya tsakanin sassa daban daban, da kawo cikas ga ayyukan masana'antu da na samar da kayayyaki na duniya, da ma raunana imanin da ake nunawa kasuwar duniya. Lamarin da ya kawo barazana mai tsanani ga farfadowar tattalin arzikin duniya, da kafa shinge ga yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Takardar bayanin mai taken "Matsayin kasar Sin kan shawararin ciniki tsakanin Sin da Amurka" ta nuna cewa, bisa sabon matakin da Amurka ta dauka kan kara sanyawa kayayyakinta harajin kwastam, Amurka ta sanya takunkumi ga wasu kamfanonin kasar Sin ciki har da Huawei bisa hujjar wai saboda tsaron kasa. Lamarin da zai kara lahanta muradun bangarori daban daban, don haka kasar Sin ta nuna matukar rashin yarda kan batun.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China