Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#Takaddamar cinikin Sin da Amurka#Takardar bayani ta bayyana yadda Amurka ta saba alkawarinta har sau uku a tattaunawar ciniki a tsakaninta da Sin
2019-06-02 12:05:51        cri
Takardar bayanan gwamnatin Sin kan matsayin da ta dauka yayin tattaunawar ciniki tsakaninta da Amurka da aka fitar a yau ta bayyana cewa, bayan da aka fara yin tattaunawar a watan Febrairu na shekarar 2018, kasashen biyu sun cimma daidaito kan yawancin batutuwan da suka tattauna a kai, amma ana fuskantar wasu matsaloli, dukkansu sun faru ne domin Amurka ta saba alkawarinta.

Takardar ta bayyana cewa, a watan Maris na shekarar 2018, gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da rahoto mai lamba 301 ga kasar Sin bayan da aka fara yin tattaunawar ciniki a tsakaninta da Sin har na tsawon wata daya, inda ta sanar da kara kudin harajin kwastam da kashi 25 cikin dari ga kayayyakin Sin masu darajar dala biliyan 50 da Sin ta fitar zuwa kasar Amurka. A watan Mayu na shekarar 2018, bayan kwanaki 10 kawai da bangarorin biyu suka gabatar da hadaddiyar sanarwar cimma daidaito kan magance yin takaddamar ciniki a tsakaninsu, gwamnatin kasar Amurka ta sabawa daidaiton da aka cimma, da sanar da ci gaba da daukar matakan kara kudin harajin kwastam. A watan Mayu na shekarar 2019, Amurka ta zargi kasar Sin da mayar da matsayinta a koma baya, sa'an nan Amurka ta daga kudin harajin kwastam daga kashi 10 zuwa kashi 25 cikin dari kan kayayyakin Sin masu darajar dala biliyan 200 da Sin ta fitar zuwa kasar Amurka, kana ta sanar da daukar matakan kara kudin harajin kwastam na sauran kayayyakin Sin masu darajar dala biliyan 300. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China