Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta samu ci gaba sosai a bangaren yawon bude ido a ciki da wajen kasar
2019-05-31 11:13:10        cri

Ma'aikatar kula da yawon bude ido da raya al'adu ta kasar Sin, ta ce a shekarar 2018, Sinawa sun yi tafiye-tafiyen da ya kai miliyan 149.72 zuwa kasashen ketare, adadin da ya karu da kaso 14 a kan na shekarar da ta gabace ta.

Wani rahoto da ma'aikatar da fitar a jiya, ya ce jimilar tafiye-tafiyen da suka yi a cikin kasar kuwa, ya kai biliyan 5.5, wanda ya karu da kaso 10.8.

Har ila yau, ziyarar da masu yawon bude ido na kasashen ketare suka yi a kasar Sin, ya kai miliyan 141.2 a bara, adadin da ya karu da kaso 1.2.

A cewar rahoton, bangaren yawon bude ido na kasar ya samu kudin shigar da ya kai yuan triliyan 5.97, kwatankwacin dala biliyan 865.22, adadin da ya karu da kaso 10.5. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China