in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da masu yawon bude ido 300,000 ne suka ziyarci bikin baje kolin lambunan shakatwa na Beijing yayin hutun farkon watan Mayu
2019-05-05 15:50:06 cri
Sama da masu yawon bude ido 320,000 ne suka ziyarci bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing, yayin hutun kwanaki 4 na farkon watan nan na Mayu.

Jami'in kwamitin shirya bikin Lei Lei, ya ce rumfar kasar Sin da rumfar kasa da kasa da rumfunan kimiyyar tsirrai da na tsarin rayuwa na zamani da kuma wajen nuna wassani na Guirui na daga cikin wuraren da aka fi ziyarta, wadanda suka samu jimilar baki 734,000 yayin lokacin hutun.

An kuma gudanar da wasu shirye- shirye da suka hada da wasannin kabilu da al'adu da kasashen yankunan tsakiya da gabashin Turai suka gabatar.

An bude bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa mai taken raya tsirrai, kyautata rayuwa' a ranar Litinin da ta gabata a gundummar Yanqing dake dab da wani bangare na babbar ganuwar kasar Sin, inda zai gudana har zuwa ranar 7 ga watan Oktoba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China