Daftarin tsare-tsare da hukumar raya kasa da sauye-sauye da sauran hukumomin Gwamnatin kasar Sin suka fitar a jiya ya ce, a bana za a zuba jarin Yuan biliyan 550 kwatankwacin sama da dala biliyan 80 a bangaren.
Wannan ya nuna karin da aka samu a kan kasa da Yuan biliyan 390 da aka zuba a bara.
Da wannan jarin, za a samu damar inganta kayayyakin more rayuwa da harkokin yawon bude ido, inda za a samar da ingantattun bandakuna, da wuraren zubar da shara da na ajiye motoci da masaukin baki.
An kuma bayyana shigar da bangarori masu zaman kansu cikin shirin, sannan za a inganta bangarorin da za a karfafawa, ciki har da hadin gwiwa tsakanin Gwamnati da bangarori masu zaman kansu.
Za kuma a karfafawa kauyuka gwiwa, ta yadda za su hada hannu da kamfanonin shirya tafiye-tafiye ta yanar gizo, sannan za a ba kanana da matsakaitan kamfanonin shirya tafiye - tafiye tallafin kudi.
Daftarin ya kuma yi hasashen cewa, a bana, tafiye-tafiye zuwa kauyuka zai kai biliyan 2.5, inda zai samar da Yuan trillion 1.4 tare da amfanawa mutane kusan miliyan 9. (Fa'iza Mustapha)