Kungiyar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasa da kasa ta MDD, wato UNWTO a takaice mai hedkwatarta a Mdrid na kasar Sifaniya, ta bayar da rahoto a kwanan baya cewa, a shekarar 2017, masu yawon shakatawa da suka fito daga kasar Sin ne ke kan gaba wajen ba da gudummowa ga kasuwar yawon shakatawar kasa da kasa.
Rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2017, an samu karuwar kasuwar yawon shakatawa a kasashen ketare a duk duniya, wanda hakan ya nuna cewa, an samu farfadowar tattalin arzikin duniya, kuma bukatun mutane a fannin na karuwa sosai. Rahoton ya nuna cewa, yawan kudin da Sinawa suka kashe wajen yawon shakatawa a kasashen ketare ya kai dallar Amurka biliyan 258. Da haka kasar Sin ta kai matsayin farko a ba da gudumowar bunkasa kasuwar yawon shakatawa ta kasashen ketare, inda kasar Amurka ke biye mata da kudi har dala biliyan 135.
Bisa kididdigar da UNWTO ta yi, yanzu haka sana'ar yawon shakatawa ta samar da guraban ayyukan yi kimanin kashi 1 cikin 10 bisa na duniya, adadin da ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. (Bilkisu)