in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen Sin da suka yi yawon bude ido a cikin gida a yayin hutun murnar kafuwar sabuwar kasar Sin ya zarce miliyan dari bakwai
2018-10-08 10:31:31 cri
Bisa alkaluman da cibiyar nazarin harkokin yawon bude ido ta kasar Sin ta bayar, an ce, yayin hutun murnar kafuwar sabuwar kasar Sin, wato daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Oktobar bana, jimillar mutanen kasar da suka yi yawon shakatawa a cikin gida ta kai miliyan 726, adadin da ta karu da kashi 9.43 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Kana, yawan kudin shigar da aka samu daga fannin yawon shakatawa a bana ya zarce Yuan biliyan 599, wanda ya karu da kashi 9.04 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.

A yayin hutun murnar kafuwar sabuwar kasar Sin na bana, an nuna himma da kwazo wajen raya sana'ar yawon shakatawa a sassa daban-daban na kasar, musamman ma wurare masu nuna tarihin juyin-juya-halin kasar da wuraren karkara da sauransu. Kazalika, hutun na bana na dab da bikin girbin amfanin gona na farko na kasar Sin, al'amarin da ya sa aka ci gaba da gudanar da bukukuwan yawon shakatawa na nuna al'adun yankunan karkara don murnar samun girbin amfanin gona mai armashi a bana. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China