Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fahimci matsayin da Sin ke dauka a takaddamar cinikayya da tattalin arziki dake tsakaninta da Amurka
2019-05-23 11:30:21        cri
Jiya ne mambar majalisar gudanarwa kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) da aka yi a Bishkek, inda ya shedawa manema labarai cewa, takaddamar cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka ya jawo hankalin kasashen duniya kwarai. Ya kuma bayyanawa ministoci a yayin taron cewa, kasashen biyu sun gamu da cikas a yayin shawarwarinsu, saboda yadda Amurka ta kasa daidaita batutuwan da Sin ke mai da hankali a kai. Mista Wang ya jaddada cewa, matakin da Sin ke dauka na kiyaye muradunta ya dace da doka, kuma tana kokarin kiyaye ka'idar dangantakar kasa da kasa da ma tsarin yin ciniki cikin 'yanci. Abin da Sin ta bayyana ya samu amincewar ministocin. Kuma sanarwar da taron ya fitar ta nuna cewa, ya kamata mambobin kungiyar su yi watsi da daukar matakai na kashin kai da manufar kariyar cinikayya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China