Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: ya fi kyau 'yan siyasar Amurka su bar sauran kasashe su taimakawa Afirka yadda ya kamata
2019-05-22 20:28:58        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Laraba a nan Beijing cewa, idan wasu daga kasar Amurka na son kula da kasashe masu tasowa, to ya fi kyau su ba da taimako na a-zo-a-gani. Amma idan ba za su iya ba, zai fi kyau su bar sauran kasashe su taimakawa kasashen na Afirka su raya kansu.

Rahotanni na cewa, dan majalisar wakilan Amurka Brad Sherman, yana yunkurin zartas da "shirin dokar tarkon basussukan kasar Sin", don taimakawa wasu su fita daga tarkon basussukan da kasar Sin ta jefa su. Kana wasu jami'an Amurka da 'yan majalisar kasar sun zargi kasar Sin cewa, wai da ta inganta tasirinta a Afirka ta hanyar aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", ta haka wasu kasashen Afirka sun fada cikin tarkon basussuka, lamarin da ya kawo illa ga ikon mulkinsu, da kuma ci gabansu mai dorewa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China