Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka da ta saurari kiraye-kiraye na gaskiya bayan da kamfanonin takalma suka kalubalanci karin haraji
2019-05-22 20:25:27        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce kasar sa na kira ga kasar Amurka, da ta saurari kiraye-kiraye na gaskiya a cikin gida, bayan da kamfanonin sarrafa takalma, da masu dillancin su na Amurkar, suka kalubalanci karin haraji kan hajjojin Sin da ake shigarwa Amurkar.

Lu Kang ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai da aka gudanar, yana mai cewa kamfanonin sarrafa takalma na Amurka sama da 170, sun yi gargadi game da mummunan sakamakon da zai iya biyo bayan karin haraji kan hajjojin Sin.

Cikin wata wasika da kamfanonin da suka hada da Adidas, da Nike da PUMA suka aike ga shugaban Amurka Donald Trump, sun ce wannan karin haraji zai zamo wata babbar masifa ga masu sayayya, da ma tattalin arzikin kasar baki daya.

Ba dai wannan ne karon farko da kamfanonin kasar Amurka suke nuna adawa da karin harajin ba. Don haka Lu Kang ya ce, hakan wata alama ce dake nuni ga rashin gamsuwar sassan 'yan kasuwar Amurka da wannan mataki na gwamnatin su, wanda ya haifar da shiga takaddamar cinikayya mai muni. Jami'in ya ce babu wata nasara da wannan jayayya za ta haifar, kamar dai yadda tsagin Sin ya dade yana bayyanawa, cewa karin harajin zai cutar da Amurkawa da kamfanonin su baki daya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China