![]() |
|
2019-05-21 20:36:15 cri |
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Talata cewa, ma'anar yin ciniki domin samun moriyar juna ita ce, samun moriyar juna, da daidaito na moriya a kasuwanni. Kuma kuskure ne a ce kasar Amurka ta kwashi asara yayin huldar cinikayya a tsakaninta da kasar Sin. Don haka ba zai yiwu a bukaci samun adalci a ko wane bangare, a yayin tattaunawa kan yarjejeniyar ciniki ba. Sai dai ya zama tilas a samu daidaito, da adalci, da moriyar juna a tsakanin kasashen 2.
Kwanan baya, shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana a lokacin da yake zantawa da manema labaru cewa, kafin tattaunawa a tsakanin Amurka da Sin, ya taba gaya wa Sin cewa, ba zai yiwu a samu adalci tsakanin Amurka da Sin cikin yarjejeniyar ciniki ba. Sakamakon abubuwan da kasar Sin ta yi a baya, ya sa ya zama tilas yarjejeniyar ta fi amfanar Amurka. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China