Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan kasuwa na ketare sun nuna karfin zuciya kan kasar Sin
2019-05-21 20:31:07        cri

Kwanan baya, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, yadda Amurka ta kara dora kudin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke sayarwa Amurka, ya sanya kamfanonin jarin waje yin kaura zuwa kasar Viet Nam, da sauran kasashen Asiya daga kasar Sin. Dangane da wadannan kalamai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Talata cewa, 'yan kasuwa na ketare sun nuna karfin zuciya kan kasar Sin.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing, Lu Kang ya nuna cewa, yadda Amurka ta keta ka'idojin cinikayya ta kawo matsala ga kasar Sin da ma kasuwannin kasa da kasa, ciki had da Amurka. Amma a karshe dai kamfanoni suna zuba jari bisa hasashensu kan makomar tattalin arziki. Lu Kang ya jaddada cewa, kamar yadda kasar Sin take yi, tana maraba da kamfanonin jarin waje da su zuba jari a kasar, tare da yin hadin gwiwa domin samun moriyar juna. Za ta kuma ci gaba da samar musu yanayin kasuwanci da na zuba jari mai daidaito, da adalci, kuma ba tare da rufa-rufa ba, inda za su cimma manufarsu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China