Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Matakin da Amurka ke dauka na kashin kanta ya kawo cikas ga shawarwari tsakanita da kasar Sin
2019-05-17 10:15:47        cri
Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Mista Gao Feng, ya ce, Sin ba ta san komai game da shirin da Amurka ke yi na turo wakilanta kasar Sin don yin shawarwari da ita ba, kuma matakin da Amurkar ke dauka yanzu, ya tsananta takaddamar dake tsakaninta da Sin a fannin cinikayya da kuma kawo cikas sosai ga shawarwari a tsakaninsu.

Gao Feng ya yi wannan furuci ne yayin wani taron manema labaru da ma'aikatar cinikayya ta yi a jiya.

An ba da labarin cewa, a ranar 13 ga wata, Amurka ta sanar da kara buga haraji kan kayayyakin da Sin za ta fitarwa kasar da darajarsu ta kai dala biliyan 300, Gao Feng ya mai da martani cewa, matakin da Amurka ke dauka na neman yin babakare da matsin lamba kan sauran kasashe ya sabawa dokar cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, kuma Sin ta yi Allah wadai da wannan matuka. Ya ce idan Amurka ta ci gaba da gudanar da ayyuka yadda ta ga dama, ko shakka babu, Sin za ta mayar da martani.

Game da labarin da ake a kwanakin baya cewa Amurka za ta turo wakilanta kasar Sin don yin shawarwari, Mista Gao Feng ya ce, yanzu Sin ba ta san komai game da wannan batu ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China