Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakamakon bincike da kasashen Turai suka samu ya wanke kamfanin Huawei daga zargin da aka yi masa
2019-05-20 20:22:52        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, sakamakon bincike da kasashen Turai suka samu, ya wanke kamfanin Huawei daga zargin da aka yi masa, kana kuma ya tono yunkurin kasar Amurka, na cin zalin kamfanonin sauran kasashe bisa karfin gwamnati.

Rahotanni daga kafofin yada labaru na kasar Jamus sun ce, bayan da kasashen Birtaniya, Jamus da kungiyar tarayyar Turai wato EU, suka shafe shekaru da dama suna bincike, a karshe dai ba su gano inda kamfanin Huawei ya yi kutse cikin kayayyakinsu ba, amma kullum na'urorin da kamfanin Cisco na Amurka ya kera kan fuskanci barazanar tsaro. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China