Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka da kada ta raina matakinta kan batun harajin kayayyaki
2019-05-14 19:48:29        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya yi kira ga Amurka da kada ta raina kudurin kasarsa na kare muradunta, yayin da Amurkar ke barazanar kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin.

Geng ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake mayar da martani, biyo bayan barazanar da Amurka ta yi na kara sanya haraji kan kusan dukkan kayayyakin kasar Sin dake shiga kasar ta Amurka. Sai dai jami'in ya ce kasar Sin ba yaki take neman tayarwa ba, amma ba ta tsoron yakin.

Haka kuma kasar Sin ba za ta mika wuya ga matsin lambar kasashen ketare ba, kana tana da karfin kare 'yanci da muradunta.

A hannu guda kuma,Geng ya ce, sanya karin haraji, ba shi ne zai warware matsalar ba, kana yakin cinikayya illa ne ga sassan biyu.

A ranar 17 ga watan Yuni ne aka shirya wakilan Amurka kan harkokin cinikayya za su gudanar da wani taron sauraron ra'ayin jama'a kan harajin kayayyakin da ta sanyawa kayayyakin kasar Sin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China