Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka tana yunkuri samun moriya ta hanyar matsa lamba fiye da kima
2019-05-20 20:35:13        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, ba a daddale yarjejeniya a yayin tattaunawa a tsakanin kasashen Sin da Amurka kan tattalin arziki da ciniki karo na 11 ba, saboda Amurka ta yi yunkurin samun moriya maras adalci, ta hanyar matsa wa kasar Sin lamba fiye da kima. Ya ce kasashen duniya sun san sahihanci da kasar Sin ta nuna a cikin tattaunawa har karo 11 da kuma ra'ayinta. Kasar Sin ta sake nanata cewa, ba za a iya samun nasara a yayin tattaunawar ba, sai kasashen 2 sun girmama juna, sun kuma yi tattaunawa cikin adalci domin samun moriyar juna.

An labarta cewa, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a kwanan baya cewa, tuni Amurka da Sin suka tsara wata yarjejeniya, amma kasar Sin ta karya yarjejeniyar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China