![]() |
|
2019-05-14 10:14:19 cri |
Jiya ranar 13 ga wata, mamban majalisar gudanarwa kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Yi da takwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov sun zanta da manema labarai.
Yayin taron manema labarai, Mista Wang Yi ya yi bayani kan makomar shawarwarin ciniki tsakanin Sin da Amurka, na cewa, an riga an samu ci gaba na a zo a gani, duk da kasancewar mawuyacin hali da bangarori biyu suke mayar da hankli don magance su.
A cewarsa, ya kamata bangarorin biyu su gudanar da shawarwari bisa tushen adalci. Babu shakka Sin tana kiyaye ikon mulkinta da moriyar jama'arta da mutuncin al'ummarta yayin da take yin shawarwari da sauran kasashe. Sin za ta tsaya tsayin daka kan wannan ka'ida a ko da yaushe. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China