Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tuntubi Amurka a hukumance dangane da shirin doka da majalisar wakilanta ta zartas kan Taiwan
2019-05-09 10:24:08        cri

Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a jiya cewa, kasarsa ta yi Allah wadai da wani shirin doka da majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas kan yankin Taiwan a kwanan baya, har ma ta tuntubi Amurkar a hukumance.

Rahotanni na cewa, a ranar 7 ga wata ne, majalisar wakilan Amurka ta zartas da wani shirin doka, inda ta nanata kudirinta kan yankin Taiwan. Da alamun shirin dokar zai fara aiki a hukumance da zarar majalisar dattawan kasar ta zartas da shi.

Geng Shuang ya ce, shirin dokar ya saba wa manufar "kasar Sin daya tak a duniya" da kuma tanade-tanaden da ke cikin sanarwar hadin gwiwa guda 3 da Sin da Amurka suka amince. Sa'an nan shirin dokar tamkar tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Kuma banganen kasar Sin ya yi fatali da shi, ya kuma tuntubi Amurka a hukumance. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China