in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne a mai da hankali kan illolin da aka samu bayan shan maganin Oseltamivir
2020-02-02 15:25:19 cri

Kasar Sin ta fara shiga lokacin hunturu, yayin da cutar murar Flu take fara yaduwa a duk kasar. Don haka ana sayen maganin Oseltamivir sosai a kasuwa, wanda shi ne magani na farko a duniya wajen yaki da kwayoyin cutar Flu. Kwararru sun yi bayani da cewa, ana zabar maganin na Oseltamivir a gaba da kome wajen shawo kan cutar Flu, saboda yana da inganci sosai, amma dole ne a mai da hankali kan illolin da ake samu bayan shan maganin.

Illolin da a kan samu kullum sakamakon shan maganin na Oseltamivir sun hada da tashin zuciya, yin amai, samun matsala wajen narkewar abinci, ciwon ciki da dai sauransu. Kuma yawan wadanda suka samu wadannan illoli ya kai kaso 6 zuwa kaso 15. Illolin ba sa yin muni bayan an daina shan maganin, domin su kan bace. Watakila mutane kalilan kan yi kuraje a fatarsu. Ban da haka kuma, wasu sun ce, idan suka sha maganin Tamiflu, su kan ji jiri, ciwon kai, ganin abubuwan da ba sa kasancewa, yin abubuwan da bai kamata a yi ba, matukar son yin barci, damuwa fiye da kima da dai sauransu, har ma wasu sun yi bakin ciki su kashe kansu. Hukumar kula da abinci da magani ta kasar Amurka wato FDA ta taba sanar da al'umma da cewa, mai yiwuwa ne maganin Tamiflu zai haifar da tabin hankali da ganin abubuwan da ba sa kasancewa, musamman ma tsakanin kananan yara. Ta kuma shawarci likitoci da iyaye da su karanta takardar bayani a tsanake, tare da sa ido kan wadanda suka sha maganin na Tamiflu.

Da kyar mutane suke iya ganin abubuwan da ba sa kasancewa sakamakon shan maganin Oseltamivir, wanda yake da amfani sosai wajen shawo kan cutar Flu. Duk da haka kada a sha maganin ba tare da iznin likita ba, ko kuma fiye da yadda likita ya kayyade. Likitoci ne ke tsai da kudurin ko ana bukatar shan maganin ko a'a. Idan kuma likitocin sun bukaci a sha maganin na Oseltamivir, to ya zama tilas su bukaci a mai da hankali kan illolin da akan samu sakamakon shan maganin, musamman ma iyayen kananan yara da kuma na matasa, dole ne su lura da 'ya'yansu ko suna yin abubuwan da bai kamata su yi ba bayan sun sha maganin.

Har ila yau kuma, wasu da sun kamu da mura sai kawai su sha maganin na Oseltamivir ba bisa shawarar likita ba, amma maganin ba shi da amfani ko kadan a garesu. Wasu kuma su kan sha maganin fiye da kima, lamarin da zai kawo musu hadari sosai.

Shan maganin na Oseltamivir ba yadda ya kamata ba yana iya kara barazanar samun illolin bayan shan maganin, haka kuma kila yana sanya kwayoyin cutar Flu su ki jin maganin. Kwayoyin cutar Flu da ba sa jin maganin za su ci gaba da yaduwa, amma shan maganin na Oseltamivir ba zai yi amfani ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China