in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shan maganin Aspirin ba tare da iznin likita ba ya kan haifar da boyayyun illoli
2020-02-02 15:26:48 cri

Karin sakamakon nazarce-nazarce sun shaida mana cewa, shan maganin Aspirin ba tare da iznin likita ba ya kan haifar da boyayyun illoli, a maimakon amfanawa lafiyar mutane kamar yadda ake zato. Amma abin bakin ciki shi ne, a halin yanzu mutane masu yawa suna shan maganin na Aspirin ba tare da izinin likita ba , watakila da yawa daga cikinsu ba su fahimci barazanar da suke fuskanta ba tukuna.

Maganin Aspirin, wani nau'in magani ne wanda ake iya saya daga kanti ba tare da iznin likita ba. Ana yin amfani da shi ne wajen yin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya ko kuma shan inna.

Tun tuni masu nazari sun yi nuni da cewa, ko da yake shan maganin Aspirin yana iya rage yiwuwar kamuwa da shan inna, barkewar ciwon zuciya da kuma mutuwa sakamakon cuttuttukan jijjiyoyin jini da ke zuciya, amma kila za a kara fuskanci zubar jini. Hadaddiyar kungiyar kula da ciwon zuciya ta kasar Amurka da hukumar ilmin ciwon zuciya ta kasar sun yi gyare-gyare kan yadda ake shan magani a kwanan baya, inda suka shawarci wadanda shekarunsu suka wuce 70, kuma suka dade suna fuskantar barazanar zubar jini, kana ba su fama da cututtukan jijjiyoyin jini da ke zuciya, da kada su sha maganin na Aspirin ba tare da iznin likita ba.

Masu nazarin na Amurka sun tantance bayanan lafiyar Amurkawa a shekarar 2017, inda suka gano cewa, mutane masu dimbin yawa suna shan maganin Aspirin, kuma watakila wasu suna shan maganin ba tare da iznin likita ba kuma ba su san illar yin hakan ba.

A cikin wadanda shekarunsu suka wuce 70 da haihuwa, kuma ba su kamu da cututtukan jijjiyoyin jinin zuciya ba, rabinsu ne ke shan maganin Aspirin a ko wace rana domin yin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya. A cikin wadanda shekarunsu suka wuce 40 da haihuwa, kuma ba su kamu da cututtukan jijjiyoyin jinin zuciya ba, adadin ya kai kashi 1 cikin kashi 4, wato kimanin miliyan 29, wadanda kuma wasu miliyan 6.6 daga cikinsu ba su samu iznin likita ba.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, ko da yake an hana masu fama da gyambon tumbi shan maganin Aspirin cikin dogon lokaci, amma da yawa daga cikinsu suna shan maganin.

Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, ya zama dole likitoci sun tambayi yadda majiyyata suke shan maganin na Aspirin, tare da ilmantar da su amfanin maganin da kuma illar da maganin yake kawo musu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China