in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila kara cin abinci masu nasaba da ganye da tsirrai zai amfana wa lafiyar zuciya
2019-11-28 15:45:35 cri

Masu nazari daga kasar Amurka sun gano a kwanan baya cewa, watakila kara cin abinci masu nasaba da ganye da tsirrai da rage cin abincin dangin nama, da madara da fatan dabbobi da sauransu suna iya taimakawa wajen rage barazanar mutuwar mutane sakamakon ciwon zuciya, shan inna, da sauran cututtukan jijjiyoyin zuciya.

Abinci masu nasaba da ganye da tsirrai su ne wadannan abincin da aka sarrafa daga ire-iren tsirrai ko 'ya'yansu ko sassansu, kamar hatsi, dankali da danginsu, wake da abincin wake, kayayyakin lambu, 'ya'yan itatuwa, shayi da dai sauransu. Abincin dabbobi kuwa, su ne nama, kwai, amfanin ruwa, madara da abincin madara da dai sauransu.

Kungiyar nazari karkashin shugabancin kwalejin kiwon lafiyar al'umma ta Johns Hopkins Bloomberg na Amurka ta kaddamar da rahoton nazari a kwanan baya cewa, daga shekarar 1987 zuwa 2016 sun yi nazari kan tsarin cin abincin Amurkawa masu matsakaitan shekaru fiye da dubu 10 da kuma lafiyar zukatansu. Kafin a fara nazarin, wadannan mutane ba sa fama da ciwon zuciya.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, gwargwadon wadanda suka ci abincin masu nasaba da ganye da tsirrai kadan, barazanar kamuwa da ciwon zuciya, shan inna da sauran cututtukan jijjiyoyin zuciya da wadanda suka fi cin wadannan nau'o'in abinci da yawa suke fuskanta, ta ragu da kaso 16, barazanar mutuwa sakamakon wadannan cututtuka da suka fuskanta ta ragu da kaso 32, galibi dai barazanar mutuwa da suka fuskanta ta ragu da kaso 25 baki daya.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, nazarinsu ya shaida cewa, watakila ba sai mutane sun daina cin abincin dangin nama, da madara da fatan dabbobi da sauransu duka. Kara cin abinci masu nasaba da ganye da tsirrai, da rage cin abincin dangin nama, da madara da fatan dabbobi da sauransu suna iya rage barazanar kamuwa da cututtukan jijjiyoyin jini dake cikin zuciya.

Hadaddiyar kungiyar masu kula da lafiyar zuciya ta Amurka ta ba da shawarar kara cin abinci masu nasaba da ganye da tsirrai a abincin yau da kullum, amma akwai sharadi. Na farko, wato kara ci abinci masu nasaba da ganye da tsirrai iri daban daban kuma marasa sukari da yawa, gishiri, kitse, da dai makamantansu. Alal misali, ko da yake soyayyen dankali siriri da kuma cauliflower da aka dafa tare da cuku, dukkansu abinci masu nasaba da ganye da tsirrai ne, amma ba sa kunshe da abubuwa masu gina jiki da yawa, kana kuma suna cike da gishiri. Abincin da ba a sarrafa su ba, kamar danyun 'ya'yan itatuwa, kayayyakin lambu da hatsi, su suka fi dacewa ga mu 'yan Adam. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China