in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi masu juna biyu su rage shan sukari
2019-09-02 09:20:35 cri


Masu karatu, kila kun fahimci cewa, a yayin bukukuwa, mutane kan taru, a ci a kuma sha, har ma bayan irin wadannan abubuwan, kullum mutane da dama su kan je ganin likita da yak ware a fannin abinci masu gina jiki, daga cikinsu, yawancinsu masu juna biyu ne wadanda yawan sukuri da ke cikin jininsu ya wuce yadda aka kayyade. Kwararru sun yi nuni da cewa, idan ha rana son rage yawan sukari da ke cikin jini, akwai bukatar masu juna biyu su rage shan sukari, su ci abinci ta hanyar da ta dace, tare da kara motsa jiki.

Miao Miao, kwararriyar likitar abinci mai gina jiki a asibitin kiwon lafiyar mata da kananan yawa na birnin Nanjing, babban birnin lardin Jiangsu a kasar Sin, ta yi bayani cewa, a yayin da ake murnar bukukuwa, masu juna biyu su kan ci abinci iya cinsu, ba sa mai da hankali kan cin abinci ta hanyar da ta dace. Da yawa daga cikinsu su kan sauya salon rayuwarsu a lokacin bukukuwan. Su kan ci abinci fiye da yadda ya kamata. Hakan a wasu lokutan ma har ba sa iya yin barci yadda ya kamata. Sun kuma rage motsa jiki saboda haduwa da abokai da dangogi. Dukkan wadannan sauye-sauye su kan sanya abin suke dauke da shi fama da matsalar yawan sukari da ke cikin jininsu.

Idan sukari da dama na taruwa cikin jikin masu juna biyu, hakan na iya kawo illa ga lafiyarsu da ma lafiyar 'yan tayinsu duka. Miao Miao ta kara da cewa, yawan sukari da ke taruwa cikin jinin masu juna biyu ya kan kara musu barazanar kamuwa da cututtuka sakamakon samun ciki, lamarin da ya kan haifar da taruwar yawan ruwan mahaifa fiye da kima, don haka masu juna biyun su kan haifi jarirai kafin lokacin da aka yi hasashe. Har ila yau kuma, 'yan tayi su kan ci abubuwa masu gina jiki fiye da yadda suke bukata a cikin mahaifa. Masu juna biyun su kan haifi jariran da nauyinsu ya kai kilo 4 ko fiye da haka, wadanda su kan yi fama da matsalar karancin sukari a cikin jininsu.

Tabbatar da daidaiton yawan sukari a cikin jinin masu juna biyu yana da muhimmanci matuka. Abu mafi muhimmanci shi ne cin abinci ta hanyar da ta dace da kuma kara motsa jiki. Miao Miao ta ba da shawarar cewa, da farko dai, dole ne a tabbatar da cewa ana cin abubuwa masu gina jiki iri daban daban lokaci-lokaci, ma'ana kada a ci abinci fiye da yadda ake bukata", kana a ci abinci kalilan amma a ci sau da dama a ko wace rana. Dole ne a mai da hankali wajen cin hatsin da ba a sarrafa sosai ba da kuma hatsin da aka sarrafa tare. Bai kamata ba a ci 'ya'yan itatuwa nan take bayan an ci abinci. Na biyu kuma,kamar yadda likitoci suke ba da shaawara, dole ne a rika motsa jiki lokaci-lokaci ta hanyar da ta dace, kamar yin yawo, yin wasan Taichi da sauran wasannin motsa jiki sannu a hankali. Ban da haka kuma, dole na a rika binciken yawan sukarin da ke cikin jinin masu juna biyu lokaci-lokaci, a mai da hankali kan yawan sukari da ke cikin jininsu bayan cin abinci, a rubuta bayanai don likitoci su gani. Ya zama tilas a gano da wuri ko an kamu da ciwon sukari, kana a yi rigakafin kamuwa da ciwon cikin hanzari. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China