in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wajibi ne masu juna biyu su yi taka tsan-tsan wajen shan maganin tari
2019-09-02 09:25:29 cri


Tari, yana daya daga cikin alamun cututtukan da suka shafi numfashi, wanda a kan gamu da shi ne sakamakon kamuwa da cutar mura, tarin fuka, ciwon huhu, da dai sauransu. Likitoci sun yi bayani da cewa, wasu magungunan tari suna iya yin illa ga yadda sassan jikin dan-Adam ke aiki, don haka ya zama tilas masu juna biyu su yi taka tsan-tsan yayin shan maganin tari.

Wasu likitocin dake kula da lafiyar mata gami da mata masu juna biyu na kasar Sin sun yi karin bayani da cewa, wasu magungunan tari suna iya hana sassa jikin dan-Adam dake taimakawa wajen yin numfashi su ji ciwo. Idan masu juna biyu wadanda suke fama da ciwon hawan jini ko kuma ciwon zuciya sun sha irin wadannan magungunan tari, hakan na iya haddasa musu matsalar yin numfashi, tare da sanya 'yan tayin da ke cikin cikinsu fama da karancin iskar shaka da ma gamuwa da matsalar iya numfashi. Magungunan tari masu dauke da sinadarin Morphine suna iya hana 'yan tayi yin numfashi yadda ya kamata, da kawo illa ga yadda sassan jikin dan-Adam ke aiki. Har ila yau kuma, magungunan tari masu dauke da sinadarin Morphine suna hana maganin taimakawa mata wajen haihuwa ya yi aiki, lamarin da zai iya tsawaita lokacin haihuwa.

Likitocin sun ci gaba da cewa, wasu masu juna biyu suna ganin cewa, magungunan gargajiyar kasar Sin ba su da illa sosai, idan aka kwatanta da magungunan zamani, don haka idan su na tari, su kan sha maganin tarin gargajiyar kasar Sin mai ruwa-ruwa mai zaki. Amma duk da haka, wasu abubuwan da aka harhada magungunan, abubuwa ne da bai dace masu juna biyu su sha ko su ci ba. Alal misali, wasu suna iya taimakawa mahaifan masu juna biyu, lamarin da ya kan sanya masu juna biyun su haihu kafin lokacin da aka yi hasashe, ko ma ciki ya zube. Kana kuma, wasu abubuwa na iya zama guba, wadanda watakila za su kawo illa ga lafiyar 'yan tayi har ma 'yan tayin su kai ga mutuwa.

Ban da haka kuma, wasu magungunan tari na gargajiyar kasar Sin masu ruwa-ruwa masu zaki suna dauke da bawon Opium da minti, wadanda bai kamata masu juna biyu da ma matan dake shayarwa su sha ba.

Likitocin sun ba da shawarar cewa, idan masu juna biyu da kuma matan dake shayarwa suna tari, to,zama tilas su je su g likita ba tare da bata lokaci ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China