in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta musunta jita-jita da aka yi kan allurar rigakafin kamuwa da ciwo (3)
2019-10-08 07:06:13 cri

Sakamakon shekaru 70 da kasar Sin ta dauka wajen raya kasa a fannoni daban daban, ya sa ya zuwa yanzu yawan mutanen da aka yi musu allurar rigakafin kamuwa da cututtuka ya wuce kaso 90 bisa jimillar yawan mutanen kasar. Allurar rigakafin na kare mutanen Sin yadda ya kamata, amma akwai wasu jita-jita dangane da allurar rigakafin, don haka kwanan baya, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta kaddamar da wani bayanin ilmantar da jama'a cikin Sinanci da Turanci da wasu harsuna a kan shafinta na yanar gizo ta Internet, inda ta musunta jita-jita da dama dangane da yin allurar rigakafin kamuwa da cututtuka.

Wasu kan ce, annobar mura ta Flu tana adabar mutane amma ba ta yin sanadin mutuwar mutane, kana kuma yin allurar rigakafi ba zai iya kare mutane daga kamuwa da annobar Flu ba. A'a, ba haka ba ne! Hukumar WHO ta ce, annobar mura ta Flu, wata irin mummunar annoba ce, wadda ta kan yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 300 zuwa dubu 500 a duk duniya baki daya a ko wace shekara. Masu juna biyu, kananan yara, tsoffafin da ba su da koshin lafiya, da wadanda suke fama da ciwon asma ko ciwon zuciya sun fi fuskantar barazanar kamuwa da annobar. Allurar rigakafin kamuwa da annobar Flu tana iya rage yiwuwar kamuwa da annoba, tare da yin tsimin kudin magani da kudin ganin likita.

Wasu sun ce, kamuwa da cuta ya fi ba da taimako wajen kyautata yadda jikin dan Adam yake kin kamuwa da cuta, gwargwadon yin allurar rigakafi. A'a, ba haka ba ne! Hukumar WHO ta ce, allurar rigakafin ba za ta haifar da ciwo ba. Amma idan an kamu da wasu cututtuka, ko da yake an kyautata yadda jikin dan Adam yake kin kamuwa da su, su kan haddasa munanan matsaloli ga lafiyar mutane. Alal misali, idan masu ciki sun kamu da cutar bakon dauron, su kan haifi jariran da suka nakasa. Kwayoyin cutar gyambon hanta na nau'in B kan haifar da ciwon kansa a hanta. Kana kuma, cutar kyanda ta kan yi sanadin mutuwar mutane.

Har iya yau kuma, hukumar ta WHO ta yi karin bayani da cewa, ko da yake ana amfani da sinadarin Mercury cikin wasu allurorin rigakafi domin kare abinci daga lalacewa ko rubewa, amma sinadarin ba zai kawo illa ga lafiyar mutane ba. Haka zalika, babu wata alaka tsakanin yin allurar rigakafi da kuma kamuwa da ciwon Autism. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China