in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta musunta jita-jita da aka yi kan allurar rigakafin kamuwa da ciwo (1)
2019-10-08 06:59:23 cri

Sakamakon shekaru 70 da kasar Sin ta dauka wajen raya kasa a fannoni daban daban, ya sa ya zuwa yanzu yawan mutanen da aka yi musu allurar rigakafin kamuwa da cututtuka ya wuce kaso 90 bisa jimillar yawan mutanen kasar. Allurar rigakafin na kare mutanen Sin yadda ya kamata, amma akwai wasu jita-jita dangane da allurar rigakafin, don haka kwanan baya, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta kaddamar da wani bayanin ilmantar da jama'a cikin Sinanci da Turanci da wasu harsuna a kan shafinta na yanar gizo ta Internet, inda ta musunta jita-jita da dama dangane da yin allurar rigakafin kamuwa da cututtuka.

Idan an kyautata kula da tsaftar jiki da na muhalli, za a kare kai daga kamuwa da cututtuka, ba tilas ba ne a yi allurar rigakafin kamuwa da cuta. A'a! Ba haka ba ne! Hukumar WHO ta ce, ko da yake kyautata kula da tsaftar jiki, rika wanke hannu da kuma shan ruwa mai tsabta suna iya kare mutane daga kamuwa da cututtuka masu yaduwa, duk da haka wasu cututtuka masu yaduwa suna iya yaduwa. Idan ba a yi allurar rigakafin kamuwa da cuta ba, wasu cututtukan da ba safai mu kan kamu da su a halin yanzu ba, za su sake barkewa nan gaba ba da dadewa ba, kamar cutar shan-inna ko Polio a Turancen da kuma cutar kyanda.

Wasu kan ce, an ji an ce, ko da yake yanzu ba a iya tabbatarwa ba, amma allurar rigakafin kamuwa da cututtuka tana illata lafiyar mutane cikin dogon lokaci. Wasu sun rasa rayukansu ne sakamakon yi musu allurar rigakafin kamuwa da cututtuka. A'a! Ba haka ba ne! Hukumar WHO ta ce, ana iya tabbatar da ingancin allurar rigakafin kamuwa da cuta. Idan an yi allurar rigakafin, a kan ji dan ciwo a hannu ko kuma zazzabi cikin gajeren lokaci. Da wuya allurar ta haifar da mummunar matsalar lafiya. Amfanin allurar rigakafin na kare mutane daga kamuwa da cututtuka ya fi barazanar da take kawo wa lafiyar mutane. Idan babu allurar, to karin mutane za su jikkata da kuma rasa rayukansu.

Akwai jita-jitar da ke cewa, wai allurar rigakafin kamuwa da cututtukan makarau, rinku da tarin jirirai da kuma allurar rigakafin kamuwa da cutar shan inna suna haifar da mutuwar ba-zata ta jarirai sabbin haihuwa. A'a! Ba haka ba ne! A cewar hukumar WHO, babu wata alaka a tsakanin yin allurar rigakafin kamuwa da cuta da kuma mutuwar ba-zata ta jarirai sabbin haihuwa. Watakila mutuwar jarirai sabbin haihuwa ta zo daidai bayan an yi musu allurar. Kada a manta da cewa, wadannan cututtuka 4 kan kashe jarirai masu tarin yawa. Idan ba a yi wa jarirai allurar ba, za su fuskanci babbar barazanar mutuwa ko kuma nakasa a sassan jikinsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China