in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne matan da suka manyanta su yi la'akari da karfinsu na haihuwa kafin su shirya samun ciki
2019-09-02 09:18:28 cri


A halin yanzu a nan kasar Sin da ma duk duniya baki daya, mata suna kara jinkitar haihuwa, don haka ake kara samun zubewar ciki sakamakon yadda 'yan tayi suke daina girma kamar yadda ake zato. Kwararru sun tunatar da cewa, kamata ya yi matan da suka manyanta su yi la'akari da karfinsu na iya haihuwa kafin su shirya samun ciki.

A yayin wani taron kara wa juna sani kan harkokin da suka shafi haihuwa da aka shirya a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin, Wang Wei, mataimakiyar darektar sashen yaki da cututtukan da suka shafi mata a asibiti na uku na jami'ar Peking ta ce, yayin da mata suke kara tsufa, a lokacin ne kuma suke kara fuskantar yiwuwar rashin aikin kwan mace yadda ya kamata, kana kuma ingancin kwayoyin halitta na Foliiculi da ke cikin kwan mace yana raguwa, har ila yau matan suna kara fuskantar rashin girman 'yan tayi yadda ya kamata.

He Wenjie, mataimakiyar darektar asibitin kiwon lafiyar mata da kananan yara na birnin Xuzhou na lardin Jiangsu ta yi karin bayani da cewa, matan da suka manyanta wadanda aka ambata a baya su ne wadanda shekarunsu suka wuce 35 da haihuwa. Yadda shekarunsu ya wuce 35 da haihuwa ya sa su kara fuskantar yiwuwar kamuwa da cututtuka sakamkon daukar ciki. Ta kara da cewa, masu juna biyu wadanda shekarunsu suka wuce 35 da haihuwa sun fi saukin kamuwa da ciwon zuciya, ciwon sukari, ciwon hawan jiki da dai sauransu sakamakon samun ciki. Kana kuma suna kara fuskantar barazanar zubar da jini bayan haihuwa da kuma shan wahalar haihuwa. Har ila yau kuma, 'yan tayi da ke cikin cikinsu suna kara fuskantar yiwuwar gamuwa da wata nakasa a jiki.

Dangane da batutuwan shan wahalar samun ciki da saukin zubewar sa sakamakon raguwar karfin haihuwa na matan da suka manyanta , He Wenjie ta ba da shawarar cewa, idan mata da mijinta suna son samun 'ya'ya, to.kafin su shirya samun ciki, kamata ya yi su binciki lafiyarsu daga dukkan fannoni, don sanin ko za ta iya haihuwa ko kwan da take da shi yana aiki yadda ya kamata, ko matar da mijinta nata sun dace da samun ciki, a kokarin kawar da yiwuwar samun ciki amma ba za ta iya haihuwa ba. Ban da haka kuma, kamata ya yi matar da mijinta su daina shan taba da giya, su kara cin abubuwan masu gina jiki, su rika yin rayuwa ta hanyar da ta dace, su kara motsa jikunansu da kuma sakin jiki yadda ya kamata yayin da suke kokarin samun ciki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China