in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila yin zazzabi a lokacin samun ciki kan kara wa yara barazanar kamuwa da ciwon Autism
2019-05-20 17:06:21 cri

Masu nazari daga kasashen Amurka da Turai sun yi bayani a kwanakin baya cewa, akwai yuwuwar idan masu juna biyu sun yi zazzabi a lokacin samun ciki, zai kara wa 'ya'yansu barazanar kamuwa da ciwon Autism.

Masu nazarin sun tantance bayanan da suka shafi lafiyar kananan yara na kasar Norway kusan dubu 100 wadanda aka haife su daga shekarar 1999 zuwa 2009 da kuma iyayensu mata. A cikin wadannan iyaye mata, wasu kashi 16 cikin dari sun ce, sun taba yin zazzabi a lokacin samun ciki, kana kananan yara 583 sun kamu da ciwon Autism. Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, idan masu juna biyu sun yi zazzabi sau daya ko biyu a lokacin samun ciki, barazanar da 'ya'yansu suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon Autism ta kan karu da kashi 34 cikin dari, kana idan sun yi zazzabi a tsakiyar lokacin samun ciki, barazanar ta kan karu da kashi 40 cikin dari. Wadanda suka yi zazzabi sau uku ko fiye da haka bayan sun cika makonni 20 da samun ciki fa? Barazanar ta kan karu fiye da sau 3.

Masu nazarin sun bayyana cikin wata sanarwa cewa, sakamakon nazarinsu ya nuna cewa, yadda kwayoyin cuta suka kama masu juna biyu da kuma yadda jikunan masu juna biyun suka yi fama da kwayoyin cutar, dukkansu sun haifar da illa kan wasu kananan yara masu fama da ciwon Autism.

Haka zalika kuma wannan nazari ya tantance illar da maganin acetyl aminophenol da kuma maganin ibuprofen suke haifarwa kan yadda kananan yaran suka kamu da ciwon Autism. Magungunan 2, magunguna ne da a kan yi amfani da su wajen rage zazzabi. Sakamakon nazarin ya nuna mana cewa, shan maganin acetyl aminophenol bai taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon Autism ba. Dukkan kananan yara da masu juna biyu da suka sha maganin ibuprofen ba su kamu da ciwon Autism ba, amma masu juna biyu da suka sha maganin ibuprofen ba su da yawa, shi ya sa ba a iya tabbatar da amfanin wannan magani kan yin rigakafin kamuwa da ciwon Autism ba.

Kafin wannan kuma, wani nazari da aka gudanar a kasar Denmark shi ma ya nuna cewa, idan masu juna biyu sun kamu da mura ko kuma zazzabi a lokacin samun ciki, barazanar da 'ya'yansu suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon Autism ta kan karu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China