in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tilas a kare masu juna biyu daga gubar dalma domin rigakafin kamuwa da ciwon hawan jini a lokacin samun ciki
2019-05-20 17:00:50 cri

Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Australiya ya shaida mana cewa, kila dimbin sinadarin dalma a cikin jinin masu juna biyu yana iya haddasa kamuwa da ciwon hawan jini a lokacin da suka samu ciki. Kwararru sun yi kashedin cewa, ya zama tilas a kare masu juna biyu daga gubar dalma.

Ma'anar ciwon hawan jini a lokacin samun ciki ita ce, bayan cika makonni 20 da samun ciki, masu juna biyu za su gamu da matsalar hawan jini, karuwar sinadarin furotin cikin fitsarinsu, kumburin jiki da dai sauransu. Idan ciwon ya tsananta, watakila masu juna biyun za su iya gamuwa da farfadiya a bayan da suka samu ciki, ko dab da haihuwa ko kuma bayan haihuwa, lamarin da ya kan kawo barazana ga rayukansu da na 'ya'yansu. Sai dai ba a san dalilin dake haddasa hakan ba tukuna, kuma ba a iya magance matsalar ba yadda ya kamata.

Masu nazari daga Australiya sun tantance sakamakon nazarce-nazarcen kasa da kasa guda 11, inda suka gano cewa, yawan sinadarin dalma da ke jinin masu juna biyu, ma'auni mafi amfani wajen yin hasashen kamuwa da ciwon hawan jini a lokacin samun ciki ga masu juna biyu. A gudanar da bincke kan dukkan wadannan nazarce-nazarce ne kan yawan sinadarin dalma da ke jinin masu juna biyu masu koshin lafiya da kuma wadanda suka kamu da ciwon hawan jini a lokacin da suka samu ciki.

Masu nazarin sun wallafa sakamakon nazarinsu a mujallar nazarin muhalli ta kasar Amurka. Sun nuna cewa, akwai wata alaka tsakanin yawan sinadarin dalma a cikin jinin masu juna biyu da kuma kamuwa da ciwon hawan jini a lokacin samun ciki. Kana kuma idan yawan sinadarin dalma a cikin jinin masu juna biyu ya ninka sau biyu, to, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon hawan jini a lokacin samun ciki zai ninka sau biyu. Karuwar yawan sinadarin dalma kadan a jinin masu juna biyu ita ma tana iya kara wa masu juna biyu barazanar kamuwa da ciwon hawan jini a lokacin samun ciki.

Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, ya kamata a kare masu juna biyu daga gubar dalma. Haka kuma kamata ya yi a binciki lafiyar masu juna biyu da yawan sinadarin dalma ya wuce microgramme 5 cikin jininsu da ya kai milliliter 100 ta fuskar ciwon hawan jini a lokacin samun ciki. Ban da haka kuma, karuwar sinadarin Calcium a cikin jikin masu juna biyu yana taimakawa wajen rage yawan sinadarin dalma a jininsu, ta haka ana iya yin rigakafin kamuwa da ciwon hawan jini a lokacin samun ciki da kuma rage illar da sinadarin na dalma ke kawo wa 'yan tayi.

Sinadarin dalma ya dade yana yiwa mutane illa, kuma zai yi matukar wahala a fitar da shi daga jikin mutane. Gurbar dalma koda kadan ce tana iya yin illa ga lafiyar mutane.(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China