Kwararru sun yi nuni da cewa, kamata ya yi a sha sinadarin Calcium bisa bayanan likitoci. Jariran 'yan kasa da watanni 7 a duniya, ba sa bukatar sinadarin Calcium da ya kai milligram dari 3 zuwa dari 4 a ko wace rana, kana kananan yara da shekarunsu suka wuce 1 amma ba su kai 5 da haihuwa ba suna bukatar sinadarin Calcium milligram dari 6 zuwa dari 8 ne kawai a ko wace rana, wadanda shekarunsu suka wuce 4 amma ba su kai 15 a duniya ba kuma suna bukatar sinadarin Calcium milligram dari 8 zuwa dubu 1 ne kawai a ko wace rana. Baligai kuma fa? An ba da shawarar cewa, mata da maza baligai bai kamata su sha fiye da milligram dubu 2 na sinadarin Calcimun a ko wace rana ba. Watakila shan sinadarin Calcium fiye da yadda muke bukata zai kawo cikas ga shiga wasu sinadarai marasa yawa cikin jikinmu, kana kuma zai haifar da matsalar duwatsu a koda. Har ila yau kuma sakamakon yadda hanta da kodar tsofaffi ba sa aiki yadda ya kamata, ya sa jikin tsoffafin ba su iya shigar da magunguna da sarrafa su kamar yadda matasa suka yi, shi ya sa ya zama tilas tsoffafin su mai da hankali sosai wajen shan sinadarin Calcium, ya kamata su sha sinadarin Calcium milligram dubu 1 da dari 2 zuwa dubu 1 da dari 5 ne kawai a ko wace rana. (Tasallah Yuan)