in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko sinadaran Bitamin, abubuwa masu gina jiki ne?
2019-04-23 08:17:13 cri
Masu karatu, ko kun taba shan magani fiye da yadda likita ya kayyade domin shawo kan cututtuka? Ko kuna shan abubuwa masu gina jiki domin kiwon lafiya? Hakika dai, akwai rashin fahimta a wasu fannonin rigakafin cututtuka da kuma kwion lafiya. Yau bari in gabatar muku wasu daga cikin wadannan fannoni.

Ko sinadaran Bitamin, abubuwa masu gina jiki ne?

Wasu da dama suna mayar da sinadaran Bitamin kamar abubuwa masu gina jiki. Amma ba su san cewa, akwai bambanci a tsakanin mutane wajen shan sinadaran Bitamin ba. Alal misali, wadanda suk kamu da mura suna iya shan sinadarin Bitamin C kadan. Wadanda su kan sha giya kuma, suna iya shan sinadarin Bitamin B6. A kan yi amfani da sinadarin Bitamin B6 wajen yin rigakafin taruwar kiba da yawa a kewayen hanta, sakamakon muhimmiyar rawa da yake takawa wajen shigar da kiba da furotin. Haka zalika kuma, masu sha'awar motsa jiki suna iya shan sinadaran Bitamin B1 da Bitamin C domin kara sinadaran da mutanen suka rasa sakamakon yin gumi da yawa. Kananan yara wadanda suke girma a ko wace rana kuwa, ya fi kyau su sha sinadarin Bitamin D, saboda abincin da suke ci a ko wace rana ba shi da isasshen sinadarin, ba su iya shigar da sinadarin ta hanyar cin abinci.

Kwararru masu ruwa da tsaki sun yi nuni da cewa, akwai iyakar sinadaran Bitamin da jikin 'yan Adam ke bukata. Idan wani ya sha sinadaran Bitamin fiye da yadda yake bukata, zai iya zame masa guba. Alal misali, shan sinadarin Bitamin A fiye da yadda ake bukata na iya haddasa rashin jin dadi, ciwon kai, yin amai, jin kaikayi a fata, rashin ganin abubuwa sosai ba, da kumburin hanta. Ban da sinadarin Bitamin A, shan sinadarin Bitamin D fiye da yadda ake bukata ka iya haddasa yin fitsari da yawa da kuma taurin wasu sassan kayayyakin cikin dan Adam. Har ila yau kuma, shan sinadarin Bitamin E fiye da yadda ake bukata, yana iya kawo barazanar zubar jini. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China