in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauraren kide-kide yana taimakawa wajen sassauta matsalar jin kara a cikin kunne
2017-05-15 13:30:44 cri

Wasu mutane suna fama da matsalar jin kara a cikin kunne. Kwanan baya, an tabbatar da amfanin sauraren kide-kide wajen sassauta wannan matsala.

Matsalar jin kara a cikin kunne da muka ambato a nan, na nufin jin kara cikin kunne amma ba tare da wani tushe na samuwar karar zuwa kunne ba.

Wata cibiyar nazarin ba da jinya ta hanyar kide-kide ta kasar Jamus, ta fidda wata sanarwa a kwanan baya, wadda ke cewa a baya, cibiyar ta ba da jinya ta hanyar sauraren kide-kide ga wadanda suke fama da matsalar jin kara a cikin kunne ta dogon lokaci.

Tun daga shekarar 2013 har zuwa yanzu, cibiyar ta ba da jinya ga wadanda suke gamuwa da wannan matsala ba zato ba tsammani. Binciken sassan jiki ta amfani da wasu na'urorin nukiliyar maganadisu ya nuna cewa, jinyar sauraren kide-kide ta amfana wa kwakwalwar masu fama da matsalar.

Binciken sassan jiki ta amfani da wasu na'urorin nukiliyar maganadisu da cibiyar ta gudanar, ya shaida cewa, cibiyar ta dauki kwanaki 5 tana ba da jinyar sauraren kide-kide ga wasu mutane 40, wadanda suka gamu da matsalar jin kara a cikin kunne ba zato ba tsammani. Bayan jinyar, mutanen da yawansu ya kai kusan kaso 85 cikin dari sun nuna cewa, jinyar sauraren kide-kide ta sassauta matsalarsu ta jin kara cikin kunnensu, sun kuma kyautata kwarewarsu ta sakin jiki da kansu.

Amma dole ne a lura da cewa, jinyar sauraren kide-kide da cibiyar nazarin ba da jinya, ta hanyar kide-kide da kasar Jamus take bayarwa, ba ta takaita ga masu fama da matsalar saurare kide-kide kawai ba ne, a maimakon hakan, cibiyar tana hadawa ba da horo kan sauraren amo da ba da horo ta fuskar tunani baki daya.

To, ko yaya cibiyar ta ba da jinyar sauraren kide-kide ke gudanar da aikin ta? Da farko ta yin amfani ne da injin sarrafa amo wajen fito da wata irin kara, da ta yi kama da karar da masu fama da matsalar suke ji a cikin kunne, sai kuma ta sanya karar cikin kide-kiden da take sanyawa masu fama da matsalar, a kokarin horas da jin su, da su sarrafa shi, da kyautata kwarewarsu ta tinkarar jin kara cikin kunnensu.

Ban da haka kuma, likitoci na bukatar masu fama da matsalar su samun aikin horaswa na sauraren amo, a kokarin farfado da sassan kwakwalwarsu na musamman, wadanda ba su aiki yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China