in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a gano da kuma ba da jinya cikin lokaci idan kananan yara sun gamu da matsala wajen saurara
2017-05-08 15:52:33 cri

Ranar 3 ga watan Maris na ko wace shekara, rana ce ta kunne ta kasar Sin. A bana, lokitocin kula da kunnuwa da hanci gami da makogwaro sun bada shawarar cewa, idan kananan yara sun gamu da matsala wajen sauraro ko ji, ya dace a gano matsalarsu cikin lokaci, a kuma yi masu jinya kan lokaci, yadda za su warke da wuri, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiyar kananan yara.

Ma'anar matsalar sauraro ko ji, wadda aken kira masu ita da kurame, ita ce samun matsalar sauraro sakamakon dalilai da dama, ta yadda masu ita ba sa iya ji ko kadan, ko kuma ba sa ji sosai. Li Jianmin, kwararre na a fannin likitanci kunne da hanci da makogwaro na asibitin jami'ar Qinghai na kasar Sin ya yi bayanin cewa, yadda kananan yara suke jin murya da amo yana taka muhimmiyar rawa yayin da suke koyon yin magana, ilmi da shiga harkokin zamantakewar al'ummar kasar. Matsalar sauraro kan kawo illa ga yadda suke yin magana, har ma wasu kan zama bebaye sakamakon rashin ji.

Li Jianmin ya bayyana cewa, akwai dalilai da dama da suke kawo illa ga kwarewar jarirai ta jin murya. Gadon dabi'un halitta yana daya daga cikin muhimman dalilan. Kuma hanya mafi dacewa da ake bi wajen magance gadon matsalar saurara ita ce tacewa, da kuma yin rigakafi kafin samun ciki, da kuma kafin haihuwar jarirai. Ya ce ya fi kyau namiji da matarsa su je asibiti don tantance ko suna dauke da dabi'un halitta na kurumta kafin matar ta samu ciki, da ma kuma kafin ta haihu, dole ne a yi mata bincike.

Wasu kwararrun ilmi a fannin kunne da hanci da makogwaro sun nuna cewa, iyawa sauraro ta wasu kananan yara bebaye na raunana ne, saboda ba a tantance su cikin lokaci ba. Ko da yake wasu iyaye kan gano cewa, 'ya'yansu ba su iya sauraro ko ji, amma ba sa amincewa da hakan, kuma ba su so a yi wa 'ya'yansu bincike. A karshe dai lokaci mafi dacewa na ba da jinya ya wuce ga wadannan kananan yara.

Galibi dai, kafin shekarun kananan yara sun kai 4 a duniya, su kan koyi yin magana, lokacin da ya fi dacewa wajen ba da jinya ga wadanda suke fama da matsalar sauraro. Kamata ya yi iyayensu su taimaka wajen yin bincike kan lafiyar jarirai sabbin haihuwa. A tace wadanda suke fama da matsalar sauraro cikin lokaci, sa'an nan a ba su na'urar sauraro, a fara aikin horaswa na farfado da jin su, da sauran taimakon da suka wajaba.

Yanzu haka na'urorin lanturoni suna samun karbuwa sosai a duniya, kuma kananan yara da yawa ba sa yin amfani da kunnensu yadda ya kamata. Dangane da hakan, kwararrun ilmin kunne sun yi gargadi da cewa, duk da yin karatu, ko kuma yin harkokin nishadi, bai dace a yi amfani da kunne fiye da kima ba. Har ila yau kuma kada a yi amfani da abin jin sauti na sanyawa a kunne fiye da rabin awa a ko wace rana, kuma ya fi kyau a yi amfani da sifikun na'urorin lantarki kai tsaye, amma a rika dan rage muryar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China