in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata ba a daina yin yawo ko hawan keke sakamakon gurbatar iska
2017-04-24 14:51:38 cri

Kowa na sane da cewa, motsa jiki yadda ya kamata yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon sukari, ciwon zuciya, ciwon sankara da dai sauransu. To, ga wadanda suke rayuwa a birane, yin yawo da kuma hawan keke da sauran hanyoyin zirga-zirga marasa gurbata muhalli su ne hanyoyin da suke bi wajen motsa jiki. Duk da haka akwai wani abu wanda yake adabar su sosai, wato idan akwai gurbatar iska a birane, shin kamata ya yi mazauna biranen su dakatar da motsa jiki ta wadannan hanyoyi?

Kwanan baya ne wata kungiyar nazari ta kasa da kasa ta kaddamar da rahotonta a shafin yanar gizo na mujallar "ilimin likitanci dangane da yin rigakafin kamuwa da cututtuka" ta kasar Birtaniya, inda a cewarta, a yawancin lokaci, ko da cikin biranen da akwai gurbatar iska, yin yawo da kuma hawan keke yadda ya kamata sun fi ba da taimako wajen kiwon lafiyar mazauna biranen, gwargwadon illar da shakar gurbatar iska yayin da ake motsa jiki ke haddasawa.

Wannan kungiyar nazari ta kasa da kasa karkashin shugabancin masu nazari daga jami'ar Cambridge ta Birtaniya, sun tantance bayanan lafiyar dan Adam da aka samu cikin nazarce-nazarce da dama da aka gudanar a baya, a kokarin sanin illar da motsa jiki cikin gurbatar iska, da kuma shakar gurbatar iska yayin da ake motsa jiki ke haifarwa ga lafiyar dan Adam.

Sakamakon tantancewar ya shaida cewa, galibi dai, illar da gurbatar iska take haifarwa ga lafiyar dan Adam ba ta iya raunana amfanin da yin yawo da hawan keke suke ba da wa. Alal misali, a birnin Delhi na kasar Indiya, gurbatar iska ta fi na birnin London tsanani har sau 10, amma duk da haka muddin tsawon lokaci da mazauna wurin suka dauka wajen hawan keke a ko wace mako bai wuce awa 5 ba, sai illar da suke fuskantar sakamakon gurbatar iska ba ta kai amfanin da motsa jiki yake kawo musu ba.

Sai daya kuma, rahoton ya yi nuni da cewa, sakamakonsu, sakamako ne da suka samu bayan da suka yi nazari kan wani birni baki daya, ba su yi nazari kan mabambantan sassan wannan birni ba, kana kuma ba su yi la'akari da saurin karuwar yawan gurbatar iska cikin gajeren lokaci da kuma tarihin wani ko wata game da kamuwa da ciwo ba.

Masu nazarin sun yi kira ga magajin gari a dukkan biranen duniya, su kara yin amfani da albarkatu a fannin tsara fasalin biranensu, a kokarin bai wa mazauna wurin sauki wajen yin yawo da hawan keke, hakan zai ba da taimako wajen kyautata lafiyar dan Adam tare da rage gurbatar iska. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China